in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu ta kaddamar da shirin yaki da rashawa
2018-08-16 10:45:34 cri

A jiya Laraba gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta kaddamar da shirin gangamin yaki da rashawa, da nufin zaburar da jama'a domin su shiga a dama da su.

Gwamnatin ta ce, ta hanyar shirin gangamin wayar da kai tana son ta isarwa al'umma sakonni domin su fahimci cewa, batun yaki da rashawa al'amari ne da ya shafi kowa da kowa.

Gamayyar shirin na tabbatar da adalci, yaki da muggan laifuka, samar da tsaro da kariya wato (JCPS), wanda ya kushi mafi yawa na ministocin kasar, ya ba da fifiko wajen yaki da rashawa wanda ya yi daidai da manufar gwamnatin kasar ta nuna ba sani ba sabo game da batun kakkabe rashawa a hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, gwamnatin kasar ta tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa.

A wata kididdiga da cibiyar kyautata dangantaka tsakanin al'ummar kasar (IRR) ta gudanar a bara ya nuna cewa, kaso 78 bisa 100 na magidantan kasar ta Afrika ta kudu sun yi amanna cewa, ayyukan rashawa a Afrika ta kudu yana ci gaba da karuwa.

Gwamnatin kasar ta ce, mutane da dama suna ganin cewa, batun rashawa ya fi kamari ne a bangaren ma'aikatun gwamnati, kuma wannan shi ne abin da kafafen yada labarai a ko da yaushe suke nuna tabbaci kansa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China