in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu tana aiwatar da sauye sauye kan tsarin rabon filaye
2018-10-15 11:07:45 cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya sanar a jiya Lahadi cewa, gwamnatin kasar tana ci gaba da daukar karin matakai na aiwatar da shirinta game mallakar filaye tare da yin sauye sauye, ta yadda 'yan kasar Afrika ta kudun za su iya mallakar gonaki don kyautata makomar rayuwarsu, tare da bunkasa ci gabn tattalin arzikin kasar.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a bikin sake mayar da gonakin bakaken fata a yankin KwaZulu-Natal.

Shirin mika gonaki mai fadin kadada 4,586 ga al'ummar yankin KwaMkhwanazi, ya zo ne a daidai lokacin da hankullan jama'ar kasar Afrika ta kudu suka karkata kan kokarin da gwamnati za ta yi wajen yin sauye sauye a tsarin rabon gonaki da aka yi tun asali a kasar, in ji Ramaphosa.

A shekarun baya an kwace gonakin al'ummar KwaMkwanazi da karfin tuwo a lokacin nuna wariyar launin fata. A 'yan shekarun baya bayan nan, al'ummomi yankunan da abin ya shafa sun gabatar da kokensu ga basarake Cetshwayo na yankin KwaZulu-Natal, inda suka nemi a maido musu da gonakin nasu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China