in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tura tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta 15 ga Darfur na Sudan
2018-12-15 15:49:12 cri

A ranar 14 ga watan nan ne bisa agogon kasar Sudan, tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin ta 15 da ta 14 suka yi bikin mika aikinsu ga juna a sansanin sojojji na El Fasher dake kasar ta Sudan. Wannan ne dai karo na 14, da tawagogin sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suka yi bikin mika aikinsu ga juna a kasar ta Sudan.

Sojoji 100 na tawaga ta 15 sun riga sun isa wurin aikinsu dake Sudan cikin jirgin sama na musamman a ranar 11 ga wata, bayan saukarsu ne kuma, ba tare da bata lokaci ba suka fara aiki a wurin.

A cikin shekara daya da ta gabata, tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta 14 da kasar Sin ta tura kasar Sudan, ta kammala aikin kiyaye zaman lafiyarta cikin nasara, har ma sojojin tawagar sun samu lambar yabo daga MDD. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China