in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin da kungiya mai zaman kanta a Sudan za su ba da tallafi ga wadanda suka gamu da ambaliyar ruwa
2017-11-06 10:33:15 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Khartoum ya kaddamar da wani shirin hadin gwiwa tare da wata kungiya mai zaman kanta don ba da tallafin kayan shimfida ga iyalai 1000 wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Sudan.

Samia Mohamed Osman, ita ce darakta janar ta gidauniyar mai suna Sanad Charity Foundation, ta fada a lokacin kaddamar da shirin cewa, wannan shirin dama suna gudanar da shi ne a duk shekara, inda a ko wace shekara ofishin jakadancin kasar Sin yana tallafawa wasu daga cikin mutanen da ibtil'in ruwan sama da ambaliyar ruwa suka shafa a dukkan jihohin kasar ta Sudan.

Ta ce, shirin daya ne daga cikin shirye shiryen da ake tallafawa iyalai kusan 1,000, inda ake samar musu da tamfal, da barguna da kuma gidajen sauro.

Jakadan kasar Sin a Sudan Li Lianhe, ya bayyana hadin gwiwar dake tsakanin ofishin jakadancin da kungiyar mai zaman kanta da cewa, alamu ne dake nuna irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasar Sudan da kasar Sin.

Li ya ce, wadannan ayyukan za su taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki da inganta yanayin zamantakewa da kyautata yanayin rayuwar al'ummar kasar Sudan.

Jakadan na Sin ya nanata aniyar kasarsa da cewa, a shirye take ta samar da karin tallafi da kuma taimako ga al'ummar Sudan domin karfafa abokantakar gargajiya dake tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China