in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin ministan harkokin wajen Sin ya kai ziyara Sudan
2016-05-16 09:17:44 cri

Daga ranar 13 zuwa 15 ga wannan wata ne, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming ya kai ziyara a kasar Sudan, yayin da ya ke ziyara a kasar, ya kuma gana da shugaba Omar al-Bashir da sauran jami'an gwamnatin kasar, kana ya yi shawarwari da ministan harkokin cikin gida da na kasashen waje na kasar Kamal Eddin Ismail, wanda shi ne shawarwarin siyasa karo na bakwai da ma'aikatan harkokin wajen kasashen biyu wato Sin da Sudan suka yi a tsakaninsu, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar dake tsakanin sassan biyu, da kuma batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da suka fi jawo hankukan su daga duk fannoni.

Zhang Ming ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana son hada kai tare da gwamnatin kasar ta Sudan domin aiwatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare kuma da kara karfafa amincin siyasa da hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu yadda ya kamata.

Kana sassan biyu za su kara yin cudanya a bangaren harkokin kasa da kasa da kuma na shiyya-shiyya, ta yadda za su ciyar da huldar sada zumunta bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu gaba sannu a hankali, haka kuma kasashen biyu da jama'arsu za su amfana da wannan dangantaka.

A nata bangare kuma, gwamnatin Sudan tana da niyyar yin kokari tare da kasar Sin domin kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu a fannoni daban daban, tare kuma da kara karfafa zumuncin dake tsakanin Sin da Sudan yadda ya kamata. Ban da haka, gwamnatin Sudan ta jaddada cewa, tana fatan za ta ci gaba da nuna wa kasar Sin goyon baya a kan batutuwan da suka shafi yankin Taiwan da tekun Nanhai da dai sauransu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China