in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta aike da dakarun wanzar da zaman lafiya 100 zuwa Sudan
2018-12-11 20:23:41 cri

Kasar Sin ta aike da dakarun wanzar da zaman lafiya su 100 zuwa kasar Sudan. Ana kuma sa ran dakarun za su yi aiki ne na tsawon shekara guda.

A yau Talata ne dakarun suka bar filin jirgin birnin Beijing zuwa yankin Darfur na Sudan.

Wannan rukuni mai kunshe da sojoji injiniyoyi dai shi ne na 15 da Sin ta tura, ciki jimillar dakaru 225 da za su yi aiki a yankin na Darfur. Ana kuma sa ran rukuni na biyu na tawagar, zai tashi zuwa Sudan a ranar 18 ga watan nan na Disamba.

Ayyukan da tawagar dakarun sojojin za su gudanar sun hada da kula da na'urori, da ayyukan injiniya, da gyara gine gine, da sake gina wasu gidajen da suka lalace, da gyaran hanyoyi, da kuma filayen jiragen sama.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China