in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya sake nanata batun kauracewa kafa gwamnatin hadin gwiwa
2018-12-15 15:43:51 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya sake nanata aniyar sa ta kauracewa kafa gwamnatin hadin kan kasa tare da jam'iyyar adawa, yana mai cewa, jam'iyyar sa mai mulki wato ZANU-PF, ba za ta yi hadin gwiwa da jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta MDC ba.

Shugaban wanda ya bayyana hakan a jiya Juma'a, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Esigodini, dake yankin Matabeleland ta Kudu, ya ce ZANU-PF ta samu babban tagomashi a zaben ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata, wanda ya bata damar kame madafun iko, don haka ba za ta bukaci hadin gwiwa da wata jam'iyya ba.

Shugaba Mnangagwa dai ya lashe kaso 50.6 bisa dari, na daukacin kuri'un da aka kada a babban zaben da ya gabata, yayin da dan takarar jam'iyyar MDC Nelson Chamisa, ya samu kuri'u kaso 44.3 bisa dari. Kaza lika jam'iyyar mai mulki ta lashe kaso biyu bisa uku, na daukacin kujerun majalissar dokokin kasar.

Sai dai a nasa bangare, Mr. Chamisa da jam'iyyar sa, sun ki amincewa da sakamakon da ya baiwa shugaba Mnangagwa nasara, suna masu kira da a gudanar da tattaunawar siyasa, domin samar da gwamnatin da suka kira ta hadin kan al'ummar kasa, wadda za ta taimaka wajen ciyar da kasar gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China