in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun kundin tsarin mulkin Zimbabwe ta amince da sakamakon babban zaben kasar
2018-08-25 15:23:56 cri

A jiya Jumma'a ne kotun kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe, ta yanke hukuncin yin watsi da karar da jam'iyyar adawa ta MDC ta shigar gabanta, game da sakamakon babban zaben kasar da aka fitar. Kotun ta ce 'dan takarar jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a kasar, kuma shugaba na yanzu Emmerson Mnangagwa ne ya lashe babban zaben da aka kada a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata.

Babban alkalin kotun kundin tsarin mulkin kasar Luke Malaba ne ya karanta wannan hukunci.

Bisa dokar kasar, hukuncin da kotun kundin tsarin mulkin kasar ta yanke, shi ne na karshe. A don haka an yi hasashen cewa, Mnangagwa zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar na wa'adin shekaru biyar a ranar 26 ga wannan wata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China