in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sanda a Zimbabwe sun karfafa tsaro gabanin fara sauraron shari'ar zabe
2018-08-21 20:41:50 cri

Yan sanda a Zimbabwe sun tsaurara matakan tsaro, gabanin fara sauraron shari'ar da za a gudanar, game da babban zaben kasar da ya gabata a ranar 30 ga watan Yuli.

Ana dai sa ran kotun kundin tsarin mulkin kasar ta fara sauraron karar da jam'iyyar adawa ta MDC ta shigar a gobe Laraba. Kotun za ta saurari korafin da jagoran jam'iyyar MDC Nelson Chamisa ya shigar, yana mai neman ta soke sakamakon zaben da hukumar ZEC ta fitar, wanda ya baiwa shugaba Mnangagwa nasara, a zaben ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata.

Chamisa ya ce, an tafka magudi a zaben, don haka yana fatan ko dai a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe shi, ko kuma a sake gudanar da babban zaben baki daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China