in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da aikin horas da mataimakan unguwar zoman Afirka a lardin Zhejiang na Sin
2018-08-20 19:18:58 cri

Yau Litinin ne aka kaddamar da aikin horas da mataimakan unguwar zoman kasashen Afirka mai lakabin "mala'ikar rayuka" a birnin Wenzhou na lardin Zhejiang na kasar Sin.

Kungiyar ingiza hadin gwiwa tsakanin jama'ar kasa da kasa ta kasar Sin, da jami'ar koyar da ilmomin likitanci ta birnin Wenzhou ne suka shirya aikin cikin hadin gwiwa, a karkashin goyon bayan ofishin jakadancin kasar Ghana dake wakilci a kasar Sin, da kungiyar zurfafa amincin dake tsakanin Sin da Tanzaniya.

Za a shafe makwani biyu ana gudanar da aikin, inda daliban kasashen Afirka sama da goma, wadanda ba su taba koyon ilmomin likitanci ba, da wasu daliban Tanzaniya dake karatun ilmomin likitanci za su shiga kwas din, bisa gayyatar da aka yi musu, domin kara fahimtar ilmomin kiwon lafiyar mata da yara.

An shirya aikin ne bisa shawarar ziri daya da hanya daya, domin kara fahimtar da jama'a ilmomin dake shafar kiwon lafiyar mata da yara, tare kuma da kara zurfafa zumuncin dake tsakanin al'ummun Sin da na nahiyar Afirka. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China