in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da rahoton masana kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka
2018-09-10 18:58:51 cri

Yau Litinin a nan birnin Beijing, hukumar hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin da ofishin nazarin harkokin kasashen yammacin Asiya da Afirka na cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin suka fitar da rahoton taron masana kan hadin gwiwar sada zumunta dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a sabon zamanin da ake ciki.

A cikin rahoton, an yi bitar babban sakamakon da sassan biyu suka samu a fannonin siyasa da tattalin arziki da cinikayya da al'adu da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan kokarin da suka yi tare tun bayan da aka kammala babban taron JKS karo na 18 a shekarar 2012, kana an nuna hakikanan sakamakon da sassan biyu suka samu yayin da suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu, ban da haka, an bayyana cewa, ci gaban tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin zai samar da sabbin damammaki ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, haka kuma hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu yana da makoma mai haske.

Haka zalika, an yi nuni da cewa, ya dace sassan biyu su kara mai da hankali kan cudanya da hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni uku wato hada shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar raya kasashen Afirka ta AU nan da shekarar 2063, kasashen duniya su hada gwiwa wajen samar da kayayyaki da yunkurin raya masana'antun kasashen Afirka, da kuma yin amfani da fasahohin yaki da talauci na kasar Sin domin cimma burin kawar da talauci a kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China