in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin Sin a kasashen Afirka na taimakawa ci gaban nahiyar, in ji jami'in bankin AfDB
2018-12-04 10:43:42 cri
Babban daraktan ofishin raya gabashin Afirka da inganta hada hadar cinikayya na bankin raya Afirka ko AfDB Gabriel Negatu, ya ce jarin da kasar Sin ke zubawa a sassan nahiyar Afirka, musamman a fannonin raya ababen more rayuwa, na da tasiri matuka wajen bunkasa tattalin arziki, da inganta zamantakewar al'ummar nahiyar.

Mr. Negatu ya yi wannan tsokaci ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Litinin, a gefen taron karawa juna sani game da tattalin arzikin Afirka da aka bude a jiya a birnin Kigalin kasar Rwanda.

Ya ce jarin da sassa masu zaman kansu ke zubawa a nahiyar, musamman a bangaren sufuri da makamashi, da raya masana'antu, zai taimakawa nahiyar wajen gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin samar da yankin ciniki cikin 'yanci.

Taron na shekara shekara karo na 13, na da taken "hade sassan shiyyar Afirka da sauran nahiyoyin duniya domin ci gaban Afirka", kuma shirin MDD na samar da ci gaba, da hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD ne suka dauki nauyin gudanar da shi. Zai kuma gudana ne tsakanin ranekun Litinin zuwa Laraba, inda ake fatan ci gaba da nazarin dabarun gaggauta samar da karin ababen more rayuwa, da hade sassan shiyyar, da kau da duk wani tarnaki dake dakile zirga zirgar jama'a, da kayayyaki, da ayyukan hidimomi tsakanin iyakokin nahiyar ta Afirka. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China