in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Afirka ta kara zuba jari a bangaren matasa
2018-11-29 13:18:38 cri

Darektan ofishin kungiyar kwadago ta duniya (ILO) dake birnin Hararen kasar Zimbabwe Hopolang Phororo, ya bayyana cewa, idan nahiyar Afirka ba ta sanya matasanta cikin ayyukan masu gwabi ba, hakika nahiyar ba za ta ci gajiyar wasu damammaki ba.

Jami'in ya bayyana hakan ne yayin taron ministocin kwadago, kudi, cinikayya da masana'antu na kasashen kungiyar SADC da aka kammala ranar Laraba a Windhoek, fadar mulkin kasar Namibia.

Ya ce, muddin ana bukatar magance kalubalen da matasan nahiyar ke fuskanta, wajibi ne a kara zuba jari a bangaren matasan, da inganta manufofin kasuwar kawadgo, ta yadda za su inganta alakar masana'antu, da fito da managartan shiryen-shiryen samar da ayyukan yi.

Manufar taron na kwanaki uku dai ita ce, inganta matakan kara samar da ayyukan yi da ingancin aiki a yankin kudancin nahiyar, da kara tattaunawa matakan samar da ayyukan yi da raya tattalin arziki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China