in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta mamaye taron kwamitin sulhun MDD yayin da Cote d'Ivoire ta karbi jagorancin taron a Disamba
2018-12-04 10:16:55 cri

Afrika tana sahun gaba a cikin ajandar taron kwamitin sulhun MDD na watan Disamba a yayin da kasar Cote d'Ivoire take shugabancin taron na wata guda.

Za'a gudanar da mahawara a tsakanin kasashe mambobin kwamitin sulhun MDDr game da yadda za'a gyara barnar da tashe tashen hankula suka haddasa a yayin taron a ranar Laraba, wanda zai samu halartar babban sakataren MDD Antonio Guterres da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki, in ji jakadan kasar Cote d'Ivoire a MDD, Leon Adom.

Taron mahawarar kwamitin sulhun zai biyo bayan mahawarar da za'a bude ne wanda za ta kunshi kasashen da ba mambobin kwamitin sulhun MDD ba ne game da yadda za'a yi hadin gwiwa tsakanin MDD da hukumomi da kungiyoyin shiyya shiyya, da nufin daukar matakan rigakafin barkewar tashe tashen hankula da warware takaddama.

Baya ga muhimman batutuwan biyu da za'a kaddamar, kwamitin sulhun MDD zai gudanar da kwarya kwaryar taro ko kuma tuntuba game da batun rikice rikice a kasashen Guinea Bissau, Sudan ta kudu, yankin Sahel da kuma jamhuriyar tsakiyar Afrika, in ji Adom.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China