in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana adawa da daftarin dokar shiga jihar Tibet ta Amurka
2018-12-14 19:01:28 cri

Kwanan baya majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da daftarin dokar shiga jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, wato idan gwamnatin kasar Sin ta hana wasu jami'an Amurka su shiga Tibet, to ita ma gwamnatin Amurka za ta hana jami'an kasar Sin masu mukamantan mukamun jami'anta shiga kasar ta Amurka, kan wannan batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, dokar da Amurka ta zartas ba ta kalli hakikanin yanayin da ake ciki ba, kuma hakan tsoma baki ne a cikin harkokin gidan kasar Sin, haka kuma ta sabawa babbar ka'idar daidaita huldar kasa da kasa, a don haka kasar Sin ta yi adawa da dokar, kuma ta riga ta sanar da kasar Amurka matsayinta kan wannan batun.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi yau, Lu Kang ya yi nuni da cewa, harkar jihar Tibet harkar cikin gida ce ta kasar Sin, bai kamata ba sauran kasashe su tsoma baki a ciki, idan 'yan kasashen waje suna so su shiga jihar, suna iya neman takardar amincewa daga wajen hukumomin da abin ya shafa.

Jami'in ya jaddada cewa, kasar Sin ta bukaci hukumomin gwamnatin kasar Amurka da su hanzarta daukar matakan da suka dace domin ganin dokar ba ta fara aiki ba, tare kuma da hana a gurgunta huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma hadin gwiwa a muhimman fannoni dake tsakaninsu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China