in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta samarwa mazauna Tibet rance kudi don soma kasuwanci
2017-05-25 09:24:34 cri

Wani bankin kasar Sin dake yankin Tibet mai cin gashin kai, zai samar da rancen kudi kimanin yuan miliyan 2 kwatankwacin dala 290,000 domin fara harkokin kasuwanci.

A cewar ofishin bankin al'umma na kasar Sin dake Lhasa, hedkwatar Tibet, wannan tsari zai amfanarwa daidaikun jama'a wajen ba su damar fara kasuwanci na hadin gwiwa, kuma wadanda suka cancanta za su samu rancen kama daga yuan 500,000 zuwa yuan miliyan 2.

Bankin adana kudi na gidan waya na kasar Sin reshen yankin Tibet ne zai bayar da rancen kudaden.

Wadanda suka kammala karatu kwanan nan za su iya samun rance domin fara gudanar da harkokin kasuwanci, kuma za'a yi musu rangwame na adadin kudin ruwan da za su biya.

Ana bukatar kammala biyan rance ne cikin shekaru 20. Wadanda ke neman rancen dole ne su gabatar da takardunsu na shedar zama 'yan asalin yankin na Tibet, kuma su mallaki kashi 30 na adadin jarin da suke bukata don fara harkokin kasuwancin.

A 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin Sin tana karfafawa Sinawa matasa gwiwa wajen shiga harkokin kasuwanci da kafa kananan masana'antu domin samun bunkasuwar tattalin arziki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China