in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Filin jirgin saman Tibet ya samu fasinjoji miliyan 2 a watanni 6 na farkon shekarar nan
2017-07-20 10:01:19 cri

Hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta yankin Tibet mai cin gashin kai dake kudu maso yammacin kasar Sin, ta sanar da cewa, ta samu yawan fasinjoji kimanin miliyan biyu da dubu 7 a watanni 6 na farkon shekarar nan ta 2017.

Hukumar ta ce, an samu karin fasinjojin da kashi 11.8 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Baki daya an samu sauka ko tashin jiragen sama kimanin 19,600 a filin jirgin saman na Tibet tsakanin watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara, adadin da ya karu sama da kashi 5.2 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kayayyakin da aka jigilar su ma sun karu da kashi 26.2 bisa 100 zuwa ton 15,900 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, in ji hukumar kula da zirga zirgar jiragen saman.

Wani jami'i ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, suna sa ran a shekarar 2017 za su samu fasinjoji kimanin miliyan 4.5, inda a watan Yuli da Agusta za'a samu karuwar fasinjoji mafi yawa dake yawon bude ido.

A halin yanzu ana iya sauka a filin jirgin saman na Tibet kai tsaye ta bangarori 72.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China