Mukaddashin babban jami'in dake nazarin yaduwar cutuka a cikin al'umma na jihar, Nuhu Bille, ya shaidawa manema labarai jiya Talata cewa, ana zargin mutane 53 sun kamu da zazzabin tun bayan barkewarsa a jihar cikin watan da ya gabata, inda ya ce mutane 4 sun mutu yayin da suke jinya a asibitin da gwamnati ta kebe.
Bisa kiddigar da aka yi a hukumance, ya ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ya zama 18, biyo bayan mutuwar ta baya-bayan nan. Ya kara da cewa wasu mutane 546 sun yi jinya sanadiyyar cutar a bana.
A ranar 22 ga watan Nuwamba ne cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Nijeriya NCDC, ta ce zazzabin lassa ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 143 a fadin kasar. An samu rahoton bullar cutar a jihohi 22 da kananan hukumomi 90, tun bayan da aka gano bullarta a ranar 1 ga watan Junairu.
A cewar hukumar ta NCDC, akalla mutane 3,016 ne ake zargin sun kamu da cutar a bana. (Fa'iza Mustapha)