in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabin Lassa ya yi sanadin mutuwar Mutane hudu a Nijeriya
2017-02-25 13:23:26 cri
An tabbatar da mutuwar wasu mutane hudu, sanadiyyar zazzabin Lassa a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

Halima Muqaddas, kwaminishar kula da harkokin kiwon lafiya a jihar Bauchi, a jiya Jumma'a, ta bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, daga karshen watan Janairu zuwa yanzu, mutane biyar ne sun kamu da cutar.

A cewarta, akwai alamar daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar na samu sauki.

Nijeriya dai ta umurci asibitocin kasar su kula da wadanda ake hasashen sun kamu da cutar yadda ya kamata, don tabbatar da gane ainihin wadanda suka kamu da cutar cikin sauri.

Gaba daya, mutane 12 ne suka mutu sakamakon yaduwar cutar ta Lassa a Nijeriya tun daga wata Nuwamban bara, a yayin da adadin ya kai sama da 80 tun bayan da cutar ta bulla a farkon shekarar da ta gabata.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China