in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata dakile annobar zazzabin Lassa ta hanyar rigakafi
2018-03-06 09:22:57 cri
Ministan lafiyar Najeriya Isaac Adewole, ya bayyana a jiya Litinin cewa, gwamnatin kasar za ta kawo karshen yaduwar cutar zazzabin Lassa a duk fadin kasar ta hanyar amfani da alluran rigakafi.

Adewole ya bayyana cewa, nan gaba kadan Najeriyar za ta amso alluran rigakafin, sai dai bai yi karin haske game da inda kasar za ta samo alluran ba.

Ministan ya shedawa 'yan jaridu a Abuja cewa, suna yin dukkan mai yiwuwa domin yakar cutar da kuma dakile bazuwarta.

A makon da ya gabata ne annobar zazzabin na Lassa ya kai kololuwa a kasar, inda ya haddasa mutuwar mutane 72, sannan aka bada tabbacin mutane 317 na dauke da kwayoyin cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi musu, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana.

An samu rahoton bullar annobar cutar zazzabin a jahohin kasar 18 tun bayan gano cutar da aka samu a karon farko a ranar 1 ga watan Janairun wannan shekara.

Jahohi uku na kudancin kasar Edo, Ondo, da Ebonyi, su ne yankunan da cutar ta fi kamari, kuma an samu kaso 85 na adadin wadanda suka kamu da cutar a jahohin uku, kamar yadda hukumar WHO ta jiyo daga hukumar yaki da yaduwar cutuka ta kasar (NCDC). (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China