in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
kungiyar SADC ta tsawaita wa'adin shirinta na wanzar da zaman lafiya a masarautar Lesotho
2018-04-25 11:38:48 cri

Taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar raya yankin kudancin Afrika SADC, ya tsawaita wa'adin shirin kungiyar na wanzar da zaman lafiya a Lesotho SAPMIL, da watanni 6.

Sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar, ta ce sabon wa'adin zai fara aiki ne daga watan Mayu mai kamawa.

Taron da aka yi jiya Talata a birnin Luanda, ya sake nazarin yanayin siyasar kasashen Lesotho da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Jamhuriyar Madagascar.

Tun a watan Decemban bara ne aka tura jami'an Shirin SAPMIL da ya kunshi sojoji 217, 162 daga cikin 'yan kasar Angola, zuwa masarautar Lesotho. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China