in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan inganta dangantakar dake tsakaninta da Amurka yadda ya kamata bisa ra'ayin bai daya da shugabanninsu suka cimma
2018-12-05 19:44:45 cri
Yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, kasarsa na fatan Amurka za ta hada kai da Sin don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba yadda ya kamata bisa matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, ta yadda za a kara samar da hakikanin moriya ga jama'ar kasashen biyu har ma ga jama'ar duniya baki daya.

Geng ya bayyana haka ne a yayin da yake ba da amsa kan kalaman sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo inda ya bayyana a jiya Talata a Brussels cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump zai bullo da wani sabon tsarin tafiyar da harkokin duniya a karkashin jagorancin Amurka. Baya ga haka, ya bayyana cewa, Amurka ba za ta amince da matakan da kasashen Sin, Iran da Rasha suka dauka na saba wa yarjejeniyoyi da dama ba, a maimakon haka, za ta dauki matakin yiwa wasu hukomimi kwaskwarima, ciki har da MDD, da IMF da kuma bankin duniya da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China