A shekarar data gabata ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da bukatar da hukumomin lafiyar kasar suka nema na ware ranar 19 ga watan Augasta a matsayin ranar ma'aikatan kiwon lafiya ta kasar Sin.
Zhang Yanling, shugaban kungiyar likitocin kasar Sin, ya ce wannan rana ta kasance a matsayin muhimmiyar rana a tarihin fannin kiwon lafiyar kasar Sin da kuma likitocin kasar.
Ya kuma bayyana cewa, ana saran bukukuwan wannan rana zasu kara daukaka matsayin kwarewar fannin kiwon lafiya.
A rahoton da aka gabatarwa taron CPC karo na 19, an yi alkawarin gudanar da sauye sauye a fannin kiwon lafiyar kasar Sin, wanda ya hada da daukar matakan inganta ayyukan hidimar kiwon lafiyar al'umma a unguwanni da kuma daga matsayin ma'aikatan dake aiki a bangaren kiwon lafiyar.