Nan da karshen shekarar nan ta 2018, kasar Habasha na fatan kaddamar da yankunan raya masana'antu 4 da kamfanonin kasar Sin suka gina a sassan kasar
Kwamishina mai lura da harkokin zuba jari a Habasha Belachew Mekuria ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Talata. Mekuria ya ce yankunan raya masana'antun da za a kaddamar su ne: Jimma Industrial Park, da Adama industrial Park, da Dire Dawa Industrial Park da kuma Arerti Industrial Park.
Kaza lika a cewar jami'in, Habasha ta shirya kara yawan jarin da take zubawa, a fannin kere kere, ciki jimillar ma'aunin tattalin arzikin kasar na GDP, daga kaso 5 zuwa kaso 20 cikin dari nan da shekarar 2025, a wani mataki na kasancewa kasa mai karfin masana'antu, wadda ke da matsakaicin kudin shiga a fannin tattalin arzikin ta nan da shekarar ta 2025.(Saminu)