in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun halaka sojojin Najeriya 70
2018-11-23 20:09:38 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun kaiwa bataliya ta 157 ta sojojin kasar dake yankin Melete na jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da tashin hankalin wani mummunan hari a kwanakin baya, inda suka halaka sojoji 70.

Wani jami'in soja ya shaidawa kamfanin dillancon labarai na Xinhua cewa, mayakan sun yiwa sansanin kwanton bauna ne, kuma galibin sojojin da mayakan suka halaka, ciki har da mai mukamin laftana sun fi karfin su ne bayan da suka bude musu wuta.

Rahotanni na cewa, sojoji da dama sun bace, bayan kai wannan hari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China