in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya gana da mataimakin shugaban kwamitin jam'iyyar Kwaminis na jihar Tibet na kasar Sin
2018-12-03 11:04:47 cri
Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya gana da wakilin jam'iyyar Kwaminis na Sin, kuma mataimakin shugaban kwamitin jam'iyyar Kwaminis na jihar Tibet na kasar Sin Ding Yexian da tawagarsa a birnin Dakar dake kasar Senegal.

A yayin ganawar, shugaba Sall ya bayyana cewa, kasar Senegal bisa matsayinta na kasar dake jagorantar sauran kasashen Afirka a karba-karba karkashin tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC, za ta yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta da karfafa hadin gwiwar da ake yi karkashin tsarin shawarar "ziri daya da hanya daya".

A nasa bangare, Ding Yexian ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Senegal wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kai, da ayyukan da aka tsara a gun taron koli na Beijing na dandalin FOCAC, da kuma sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Senegal, har ma tsakanin Sin da nahiyar Afirka gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China