in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Boko Haram ta fara amfani da manyan fasahohi wajen kai hari kan dakarun Nijeriya
2018-11-30 10:06:27 cri

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa, yanzu kungiyar Boko Haram ta fara amfani da manyan fasahohi wajen farwa sansanonin soji dake arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da babban hafsan sojin kasar Tukur Buratai ya fitar, ta ce yanzu Boko Haram na amfani da jirage mara matuka da mayakan haya wajen kai hare-hare, wanda ke zaman babbar barazana ga kasar.

Tukur Buratai ya ce cikin watanni 3 da suka gabata, sun lura cewa 'yan ta'adda na gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ba, inda suka kara amfani da jirage mara matuka wajen kai hare-hare kan sojoji da kuma amfani da mayakan haya baki, inda ya ce wannan babbar barazana ce dake bukatar rundunar soji ta ci gaba da bitar ayyukanta.

Ya kuma tabbatar da cewa, mayakan Boko Haram sun kai hari kan a kalla sansanonin sojoji 5 tsakanin ranar 2 zuwa 18 ga watan nan, yana mai cewa sojoji sun dakile yunkurin 'yan ta'addan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China