in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Somaliya da AU sun kafa shirin kawance don kakkabe mayakan al-Shabaab
2018-08-16 09:49:53 cri

Tawagar dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika AU da dakarun tsaron kasar Somaliya a jiya Laraba sun kaddamar da wani shirin soji na hadin gwiwa a yankin Lower Shabelle domin murkushe mayakan 'yan ta'adda na al-Shabaab.

Abdiweli Jama Hussein, babban jami'in tsaro na rundunar sojojin kasar Somaliya (SNA), ya bayyana cewa, makasudin kafa rundunar wanzar da tsaron shi ne, domin farautar mayakan 'yan ta'adda wadanda suka tsallaka zuwa yankunan arewacin kasar.

A cewar Hussein, dakarun sojojin na Somaliya da dakarun tsaron na AMISOM, sun sha alwashin kakkabe 'yan tada kayar bayan, domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar, kuma za su tabbatar da mutunta dokokin kare hakkin dan adam na kasa da kasa a lokacin gudanar da aikin hadin gwiwar tabbatar da tsaron.

Ya ce, tuni aka umarci dakarun sojojin na Somaliya da su hada kai da dakarun tsaron na AMISOM da sauran abokan hulda na rundunonin soji wajen kaddamar da zafafan hare hare kan mayakan na al-Shabaab.

Shirin wanzar da tsaron ya zo ne a daidai lokacin da jami'an wanzar da zaman lafiyar Somaliya ke ci gaba da kaddamar da ayyukansu a sassan yankunan kudancin kasar, bayan da aka samu karuwar hare haren ta'addanci a kasar ta gabashin Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China