in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci karin hadin gwiwa domin warware kalubalen samar da agaji a Somaliya
2018-04-20 10:19:55 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya (AMISOM), ta bukaci yin hadin gwiwa don warware manyan kalubalolin da suka shafi samar da agajin jin kai a kasar ta gabashin Afrika.

Abdul Diabagate, babban jami'in ofishin kula da ayyukan jin kai na AMISOM, ya bayyana bukatar samar da karin taimako wajen gudanar da ayyuka jin kai, da yin cudanya da al'ummomin yankunan dake fama da matsalolin rikice-rikice da yankunan da suke fama da matsalolin ibtila'in annoba.

Diabagate ya fada haka a lokacin taron ba da horo na wuni guda ga abokan huldarsu dake gudanar da ayyukansu a yankunan da abin ya shafa a Jowhar, babban birnin jihar HirShabelle ta Somaliya cewa, kalubalolin da suka shafi aikin samar da agajin jin kai yana bukatar a samu karin hadin gwiwa, da kuma tattaunawa tsakanin tawagar AMISOM da abokan huldarsu dake yankin.

An shirya taron ba da horon ne domin samar da karin fahimtar juna da sanin ka'idojin aikin sojoji game da ayyukan da suka shafi fararen hula tsakanin abokan aikin AMISOM da sauran jami'an dake tallafawa aikin jin kai a kasar.

Taron ya kuma zaburar da mahalartan game da muhimmancin kiyaye dokokin kasa da kasa game da ayyukan jin kai da mutunta dokokin hukumar tallafawa 'yan gudun hijira ta kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China