in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen gabashin Afrika da su kawar da cin hanci
2016-11-17 10:08:05 cri

An yi kira ga kasashen gabashin Afrika da su nuna jajarcewa cikin hadin gwiwa domin kawar da cin hanci, wanda ya kasance wani babban tarnakaki ga aiwatar da ayyukan dunkulewar shiyyar gabashin Afrika EAC. Ma'aikatan dukkan kasashe mambobi na kungiyar EAC sun kaddamar da wannan kira a ranar Laraba a birnin Arusha.

Almas Maige, shugabar kungiyar ma'aikatan Tanzaniya (ATE) ta bayyana cewa, cin hanci na karuwa a shiyyar, kuma na taimakawa ga kankare masu zuba jari.

Haka kuma, madam Rosemary Ssenabulya, shugabar kungiyar ma'aikatan kasashen gabashin Afrika (EAEO) ta jaddada wajabcin ganin ma'aikata da abokan hulda na jama'a na EAC da su jagoranci masu zuba jari da ma'aikata kan hanyar gudanar da harkoki cikin tsari na gari.

A cewar EAEO, dukkan ka'idoji kan dangantakar jama'a ya kamata su taimaka wa ma'aikatan gabashin Afrika wajen kafa zamantakewar al'umma mai armashi a wurarensu na aiki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China