in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An watsa shirye-shiryen TV na musamman biyu a kasashen Sin da Argentina a lokaci guda
2018-11-29 09:54:12 cri

Tun a yau Alhamis 29 ga wata, wato gabannin bude taron koli na kungiyar G20 a kasar Argentina, aka fara watsa wasu shirye-shiryen musamman masu taken "Kasar Argentina mai burgewa" da "Kasar Sin mai ban al'ajabi" a gidajen talibijin na kasashen Sin da Argentina a lokaci guda. Ta wadannan shirye-shiryen musamman biyu da kasashen biyu suka dauki nauyin shiryawa, jama'a masu kallo na kasashen biyu za su kara fahimtar abubuwan ban al'ajabi na kasashen juna.

A yayin bikin kaddamar da watsa shirye-shiryen da aka yi a ranar 28 ga wata a birnin Buenos Aires, babban birnin Argentina, karamin sakatare mai kula da kafofin watsa labarai na kasar Argentina Hernan Lombardi ya bayyana cewa, wadannan shirye-shiryen biyu babbar kyauta ce da ake ba taron koli na G20. Ya ce, hakika, 'yan kasarsa na sha'awar yadda kasar Sin take. Tsara wadannan shirye-shiryen TV biyu tsakanin bangarorin biyu, ya sa mun gano cewa, akwai abubuwa kusan masu tarin yawa iri daya a tsakaninmu, lallai wannan na da babbar ma'ana ga jama'ar kasashen biyu.

A jawabinsa shugaban babban gidan talibiji da rediyo na kasar Sin CMG Mr. Shen Haixiong ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba yin bayani sosai kan cudanyar al'adu daban daban, inda ya jaddada cewa, ya kamata a kara samun basira da ma darasi daga al'adu daban daban, ta yadda za a kara karfafawa jama'a gwiwa ta fuskar tunani, domin tinkarar kalubaloli daban daban da ke fuskantar bil Adama. Mr. Shen ya kuma kara da cewa, wadannan shirye-shiryen TV biyu da aka dauka cikin tsanake zai taimakawa jama'ar kasashen biyu wajen kara fahimtar juna da sha'awar dogon tarihi na al'adu na gari na kasashen biyu. Ba za a samu ci gaba a lokaci guda ba sai mun yi cudanya da ma koyi da juna.

Ban da wannan kuma Rukunin CMG da gidan talibijin da rediyo na kasar Argentina sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin kai a yayin bikin.(Mai fassara: Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China