in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU: Za a hukunta duk kasar da ta gaza biya kason tafiyar da harkokin kungiyar
2018-11-28 08:57:45 cri

Mataimakin shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka Kwesi Quartey ya ce, za a yanke hukunci mai tsanani kan duk wata mambar kungiyar da ta gaza biyan kudinta na karo-karon tafiyar da harkokin kungiyar, kamar yadda shugabannin nahiyar suka yanke shawarar hakan yayin taronsu na birnin Kigalin kasar Rwanda.

Jami'in ya ce, tsarin na daga cikin shawarar da shugabannin suka cimma game da samar da kudaden tafiyar da harkokin kungiyar, matakin da zai kai ga cimma nasarar ajandar kungiyar a fannin kudade.

Babban taron kolin shugabannin gwamnatocin kasashen kungiyar karo na 11 wanda ya gudana daga ranar 17 zuwa 18 ga watan Nuwamba a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya jaddada garkama takunkumin ne don tabbatar da cewa, kasashe mambobin kungiyar 55 sun biya kudadensu na karo-karo a kan lokaci.

Daga cikin takunkumin da za a sanyawa kasar da ta gaza biyan kudaden sun hada da, dakatar da ita kwata-kwata daga harkokin kungiyar da ma halartar duk wasu tarukan kungiyar.

Kusan rabi daga cikin adadin kasashe mambobin kungiyar dai na matakin aiwatar da shawarar samar da kaso 100 bisa 100 na kudaden tafiyar da harkokin kungiyar, da kuma kaso 75 cikin 100 na kudaden tafiyar da shirye-shiryenta da kaso 25 cikin 100 na ayyukan wanzar da zaman lafiya na kungiyar nan da shekarar 2021.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China