A cikin mutanen 17 da aka damke, akwai mazauna yankin Hong Kong guda shida, wadanda suka yi yunkurin shigo da haurin giwa babban yankin kasar Sin ta hanyar Hong Kong.
Tuni a watan Yulin shekarar 2017 da ta gabata ce, aka kama irin wadansu mutanen da ake zarginsu da fasa kwaurin haurin giwa. An dai kafa wata tawagar hadin gwiwa, karkashin babbar hukumar kwastam ta kasar, domin ta kara gudanar da bincike game da lamarin.
Tawagar ta kuma kai samame biyu, wanda ya kai ta ga damke wadanda ake zargin a watannin Yuni da kuma Yuli. An yi kiyasin cewa, bata garin sun yi sumogan kusan kilogram dubu na haurin giwa da wasu kayayyaki dake da nasaba da sassan dabbobi tun a watan Nuwamban shekarar 2017.
A shekarar 2015 ne dai gwamnatin kasar Sin ta dakatar da shigo da haurin giwa da dukkan kayayyakin masu alaka da shi, ta kuma dakatar da sarrafawa da ma sayar da haurin giwa baki daya a karshen shekarar 2017.(Ibrahim)