in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi za ta yiwa 'yan kasar miliyan 7 riga kafin cutar sankarau
2018-11-27 11:07:17 cri

Ministan lafiya da yaki da cutar kanjamau na kasar Burundi Thaddee Ndikumana ya ce, kasarsa ta shirya tsaf don yiwa 'yan kasar sama da miliyan 7 alluran riga kafin cutar sankarau, kwatankacin kaso 77 cikin 100 da daukacin al'ummar kasar.

Shirin riga kafin wanda zai gudana daga ranar 4 zuwa 13 ga watan Disamba mai kamawa, zai shafi 'yan kasar masu shekara 1 zuwa talatin da haihuwa.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, kasar ta Burundi dake yankin tsakiyar Afirka, tana daya daga cikin kasashe 26 na kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Afirka dake kan gaba wajen fama da wannan cuta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China