in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi ya fidda shirin raya kasa na shekaru 10 yayin bikin samun 'yancin kan kasar
2018-07-02 10:42:20 cri

A yayin da al'ummar kasar Burundi ke murnar cika shekaru 56 da samun 'yancin kan kasar, shugaba Pierre Nkurunziza na kasar ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta tsara shirin ci gaban kasar nan da shekaru 10 masu zuwa a yayin bikin murnar samun 'yancin kan kasar.

A sakon da ya gabatarwa 'yan kasar a Bujumbura, babban birnin kasar Burundin, Nkurunziza ya ce, wannan shiri zai fara aiki ne daga shekarar 2018 zuwa 2027, kuma wasu kwararrun masanan kasar Burundin 70 ne suka tsara shi.

A cewarsa, za'a fassara shirin raya kasar zuwa harshen Kirundi wanda shi ne mafi shahara a kasar. Kana kwararrun masanan su 70 da sauran masanan kasar za su fara tsara wani shirin raya kasar daga shekarar 2022 wanda zai kai har zuwa shekarar 2040, in ji mista Nkurunziza.

A yau Litinin ne za'a gudanar da bikin samun 'yancin kan kasar karo na 56, mai taken "Tabbatar da samun 'yancin kasa ta hanyar hada kai da yin aiki tukuru: su ne tushen ci gaba."

Shugaban kasar ya ce, bikin murnar samun 'yancin kasar zai ba da damar tunawa da 'yan mazan jiya wadanda suka yi fafutukar tabbatar da 'yancin kasar.

Shugaban na Burundi ya gargadi 'yan kasar su ci gaba da yin aiki tukuru, da tabbatar da hadin kai da kuma nuna kishin kasa don ci gaban kasarsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China