in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin: Bai dace a rika sanya batun Burundi cikin ajandar kwamitin sulhun MDD ba
2018-11-22 18:48:23 cri

Mataimakin wakilin kasar a MDD Wu Haitao ya ce, bai kamata batun kasar Burundi ya ci gaba da kasancewa cikin ajandar kwamitin sulhun majalisar ba, ganin yadda zaman lafiya ya samu a kasar.

Mr Wu ya ce, kasar Sin ta yi fahimci sanarwar da ministan harkokin wajen kasar Burundi Ezechiel Nibigira ya gabatar yayin babban taron zauren MDD na wannan shekara cewa, an samu zaman lafiya a kasar, kuma komai na tafiya yadda ya kamata.

Ministan ya ce, bai kamata a ci gaba da sanya kasarsa cikin ajandar kwamitin sulhun majalisar ba, domin yanzu ba ta da wani barazanar tsaro a yankin ko kuma a duniya.

Hu Haitoa ya ce, kasar Sin tana ganin cewa, ya kamata kwamitin sulhun MDD ya saurari Burundi, kana ya dauki mataki, da rashin nuna son kai game da yanayin da ake cikin kasar Burundi. Haka kuma ya kamata kwamitin sulhun ya gudanar da wasu canje-canje bisa ga ci gaba na baya-bayan da aka samu, ya kuma aike da sakamako mai gamsarwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China