in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi ya gana da mataimakin shugaban CPPCC Liu Qibao
2018-10-24 10:33:12 cri

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, ya gana da wakilan tawagar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, wadanda ke ziyara a kasar, karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar Liu Qibao.

Yayin ganawar da suka yi jiya a Bujumbura, fadar mulkin kasar Burundi, Liu Qibao ya bayyana cewa, a bana ake cika shekaru 55 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Burundi, kuma a cikin shekarun baya-bayan nan, huldar dake tsakaninsu ta samu ci gaba cikin sauri karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu. Ya ce kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Burundi domin kara karfafa fahimtar juna a fannin siyasa, tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu, ta yadda al'ummomin kasashensu za su samu moriya. Kana ya yi bayani kan taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing, da babban sakamakon da kasar Sin ta samu tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarimar tattalin arziki da bude kofa ga ketare cikin shekaru 40 da suka gabata, musamman ma tun bayan da aka shirya babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, da sakamakon da aka samu bayan fara aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da dai sauransu.

A nasa bangaren, shugaba Nkurunziza ya jinjinawa ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu, yana mai yabawa da dimbin sakamakon da kasar Sin ta samu tun bayan da ta fara aiwatar da manufar gyaran fuska da bude kofa ga ketare, inda ya ce kasarsa na son kara karfafa cudanya da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, ta yadda za a kara ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China