in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guraben aikin yi da kamfanin gina layin dogo na kasar Sin ya samar sun zarta dubu 72 a Kenya
2018-06-23 15:59:37 cri

Kamfanin gina hanyoyi na kasar Sin, ya ce jimilar guraben aikin yi da kamfanin shimfida layin dogo na kasar ya samar ga al'ummar kasar Kenya ta zarce dubu 72.

Rahoton da kamfanin ya fitar a jiya ya ce, yayin gina layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi, an dauki ma'aikata da adadinsu ya kai sama da dubu 46 a yankunan, yayin gina layin dogo tsakanin Nairobi da Malabar kuwa, an dauki ma'aikata sama da dubu 26 a yankunan.

Shugaban kamfanin gina hanyoyi da gada na kasar Sin Lu Shan, ya bayyana cewa, layin dogon da kamfaninsa ya gina a kasar Kenya ya taka rawar gani ga ci gaban tattalin arzikin kasar, inda har alkaluman GDP na kasar ya karu da kaso 1.5 bisa dari.

A watan Mayun bara ne aka kaddamar da layin dogo mai tsawon kilomita 480 da aka fara aikin shimfidawa tsakanin Mambasa da Nairobi a watan Disamban 2014.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China