in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Ana sa ran Afirka za ta zama babbar kasuwa a duniya
2018-11-20 20:35:56 cri

Wani rahoto da kamfanin McKinsey mai kula da harkokin gudanarwa ya fitar, ya nuna cewa, nan gaba nahiyar Afirka ce za ta kasance babbar kasuwa a duniya, sakamakon bunkasar yankin Asiya.

Rahoton ya ce, yayin da sauran sassan duniya ke samun karuwar ci gaba, kamfanonin duniya da suka bunkasa tun farko sun hada kai da takwarorinsu na Afirka wajen inganta manufofinsu, matakin da zai taimaka wajen kara samun riba cikin wasu gomman shekaru dake tafe.

Haka kuma rahoton ya zayyana wani sakamakon bincike 3,000 da kamfanin McKinsey ya gudanar, da bincike mai zurfi da tambayoyi da ya yi da fitattun 'yan kasuwa 40 na Afirka da shugabannin raya kasashe.

Rahoton ya ce, Afirka ta samu saurin ci gaba, da bunkasar mazauna birane da muhimman bukatun da ba a iya kaiwa da samar da su ba, wannan na nufin cewa, akwai damammaki na kusan triliyoyin daloli don raya masana'antun nahiyar, domin a kai ga cimma karuwar bukatun nahiyar da samar da yanayin da ya dace a kasuwannin fitar da kayayyaki na duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China