in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECA ta lashi takobin taimakawa yammacin Afrika wajen amfana daga yawan al'ummarsa
2018-11-24 16:34:41 cri

Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD ECA, ta ce a shirye take ta taimakawa yankin yammacin Afrika samun moriya daga yawan al'ummarsa.

Shugaban ofishin hukumar na yankin yammacin Afrika, Bakary Dosso, wanda ya ce ofishinsa a yanzu na shirya taron ayarin kwararru don nazari da amincewa kafa ingantacciyar cibiyar nazarin sauye-sauyen dake tattare da adadin al'umma domin ci gaban yankin, ya kuma bayyana burin cibiyar na zama ja gaba a wannan fanni a yankin yammacin Afrika.

Bakary Dosso, ya ce sun dauki wannan mataki ne la'akari musammam da sauye-sauyen adadin al'umma a yammacin Afrika, yana mai cewa, yankin ne ya dauki kaso 30 na jimilar al'ummar nahiyar, inda Nijeriya dake yankin ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar.

Ya kara da cewa, an fi samun yawan haihuwa a yankin, kuma a nan aka fi samun karuwar adadin jama'a a duniya, yayin da kuma yake zaman yankin da ake samu karuwar masu kaura, saboda yanayi na gaggawa dake haifar da matsarwar jama'a, wanda rashin tsaro ke daya daga cikin musababbabinsa

A cewar ECA, taron ayarin kwararru zai yi bita tare da amincewa nazari kan kafa cibiyar, da nufin saukaka ayyukan da hukumar ta fi kwarewa a kai, na kasancewa muhimmiyar cibiyar nazarin adadin jama'a da harkokin tattalin arziki, domin ci gaban yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China