in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci nahiyar Afrika ta kara yawan kasafin kudi ga ayyukan raya muhalli
2018-11-03 17:08:52 cri

Hukumar MDD mai kula da muhalli, ta yi kira ga gwamnatocin Afrika su kara yawan kasafin kudi ga ayyukan raya muhalli.

David Ombisi, shugaban sakatariyar ministocin muhalli na kasashen Afrika ta hukumar, ya ce karin kaso 1 a kowacce shekarar ba zai isa wajen taimakawa shawo kan matsalolin muhalli ba.

Jami'in ya shaidawa manema labarai a Nairobin Kenya cewa, ana alakanta kaso 23 na mace-mace a nahiyar, da matsalolin muhalli, inda ya ce alkaluman na Afrika sun dara na sauran yankunan duniya.

Ya kuma dora alhakin barkewa da yaduwar cututtuka a nahiyar, kan rashin isashen kudi da ake warewa bangaren muhalli.

Ya ce, sakatariyar ta lura akwai bukatar shigar da ma'aikatun lafiya da na kudi da tsare-tsare, domin taimakawa tattaunawar samar da kudi ga shirye-shiryen raya muhalli.

David Ombisi, ya ce abu ne mai muhimmanci, gwamnatocin Afrika su samar da dunkulalliyar dabarar kiwon lafiya da raya muhalli, wadda za a samar mata da isasshen kudi.

Ya ce, idan aka samar da isasshen kudi ga bangaren muhalli, jama'a za su rayu cikin koshin lafiya, domin cututtuka za su ragu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China