in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Birtaniya za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar ficewar kasar daga EU ranar 11 ga Disamba
2018-11-27 10:31:38 cri

Firaministar Birtaniya Theresa May, ta tabbatar da cewa, majalisar dokokin kasar za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar ficewar Birtaniyar daga Tarayyar Turai EU a ranar 11 ga watan Disamba.

Theresa May, ta ce yarjejeniyar da shugabannin EU suka amince da ita a ranar Lahadi, yarjejeniya ce da ta dace da Birtaniya saboda tana kunshe da matakin da al'ummar kasar suka dauka a watan Yunin 2016, lokacin da kasar ta gudanar da zaben raba gardama.

Firaminista May, ta shiga hali mai tsanani a jiya, inda ta fara kokarin shawo kan mambobin majalisar game da yarjejeniyar.

Ta shaidawa mambobin majalisar cewa, zabuka biyu ake da su, ko a amince da yarjejeniyar, ko kuma a mayar da hannun agogo baya wanda ba shi da makoma.

Jagoran 'yan adawa na jam'iyyar Labour, Jeremy Corbyn, ya bayyana yarjejeniyar ta Madam May a matsayin mara kyan tsari, yana mai cewa yarjejeniya tsakanin Birtaniya da Tarayyar Turai ta gaza.

La'akari da 'yan majalisar da dama daga Jami'iyyar Conservative na firaministan na cewa, za su kada kuri'ar kin amincewa da yarjejeniyar, masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin akwai yiwuwar yarjejeniyar ta sha kaye a wata mai zuwa (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China