in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko Birtaniya za ta fice daga EU?
2018-11-22 18:43:59 cri

Kunigyar tarayyar Turai wato EU za ta shirya wani taron koli na musamman a ranar 25 ga wata domin tattauna batun ko za ta zartas da daftarin kudurin ficewar Birtaniya daga kungiyar da ta daddale da kasar, kafin wannan, majalisar ministocin Birtaniya ta zartas da wannan daftarin kuduri mai shafuka 585, tana ganin cewa, shi ne kuduri mafi dacewa da aka daddale yayin shawarwari, kana abu mafi muhimmanci shi ne yayin taron kolin da za a kira, firayin ministar kasar Theresa May za ta fitar da wata sanarwar siyasa kan huldar dake tsakanin sassan biyu cikin hadin gwiwa da EU, wannan na nuna cewa, kasar ta Birtaniya ta shiga wani mataki mai muhimmanci matuka.

Duk da cewa, an ga Birtaniya ta bayyana cewa, za ta fice daga EU, amma ga alama, watakila ba ta son yin haka, wannan shi ma wani dalili ne da ya sa madam Theresa May ta nace ga daddale daftarin kuduri da EU kafin ficewarta daga kungiyar.

Daga abubuwan da aka rubuta a cikin daftarin kudurin, za a tabbatar da cewa, Birtaniya za ta fice daga EU bisa doka, amma hakika tana cikin kungiyar, a don haka daftarin kudurin ya nuna cewa, sassan biyu ba su so su canja halin da suke ciki yanzu, nan gaba idan sassan biyu suka fitar da sabon shiri, dole a tabbatar da cewa, ba zai kawo illa ga cudanyar jama'a da cinikin kayayyakin dake tsakaninsu ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China