in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Birtaniya sun yi shawarwari karo na 9 tsakaninsu
2018-07-30 19:58:54 cri

Yau Litinin mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da takwaransa na kasar Birtaniya Jeremy Hunt sun yi shawarwari kan tsare-tsaren kasashen biyu karo na 9 a nan birnin Beijing, kuma sun yi ganawa da manema labarai tare.

Wang Yi ya bayyana cewa, gaba daya sassan biyu suna ganin cewa, kamata ya yi su kara kyautata huldar dake tsakaninsu yayin da ake aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Haka kuma yayin shawarwarin, sassan biyu sun yi musanyar ra'ayoyi kan batutuwan dake shafar yadda za a kiyaye tsarin gudanar da cinikayya maras shinge da sauransu. Wang Yi yana mai cewa, kasar Sin za ta hada kai tare da kasar ta Birtaniya da sauran kasashen duniya baki daya domin kiyaye tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama, da tsarin cinikayya maras shinge a fadin duniya, da kuma ka'idojin hukumar WTO. Game da rigingimun cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, Wang Yi ya jaddada cewa, dalilin da ya jawo matsalar cinikayyar da Amurka ke fuskanta yana da nasaba da manufofin kasar ta Amurka ita kanta, kasar Sin tana son yin shawarwari da Amurka bisa tushen adalci da girmama juna, yin barazana da matsa lamba za su kawo illa ga huldar dake tsakanin sassan biyu.

A nasa bangare, Hunt ya bayyana cewa, kila kasar Sin za ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a cikin shekaru 20 masu zuwa, ci gaban kasar Sin zai amfanawa sauran kasashen duniya, Birtaniya tana fatan za ta kara karfafa shawarwari tsakaninta da kasar Sin, domin kara zurfafa zumunta dake tsakanin sassan biyu, a don haka gwamnatin Birtaniya tana sa ran cewa, za ta cimma burin dakile kalubale iri iri da kiyaye tsarin kasa da kasa tare da kasar Sin ta hanyar kara karfafa cudanya da hadin gwiwa daga duk fannoni tsakaninta da kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China