in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birtaniya ta bunkasa ayyukan AMISON domin wanzar da tsaro a Somalia
2018-07-02 09:59:57 cri

Birtaniya ta ba da gudunmuwar injuna 47 da za su taimaka wajen bunkasa ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika da ake kira da AMISOM a Somalia, a yakin da yake da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta al-Shabaab, a wani bangare na wanzar da zaman lafiya a kasar dake kahon Afrika.

Shirin AMISOM ya ce, manyan injunan da suka hada da tracto da tipa da sauransu, za su taimaka wajen gyaran manyan hanyoyin kai agaji, yayin da yake shirye-shiryen mika ragamar tsaro ga dakarun kasar.

Sanarwar da kwamandan sashe na 1 na shirin, Brigadier Paul Lokech ya fitar a Mogadishu, ta ce da wadanan injunan, za su iya inganta ayyukansu, sannan za su taimaka musu tare da al'ummar kasar cimma abubuwan da ake bukata a matakin farko, na shirin mika ragamar tsaron kasar.

Paul Lokech, ya ce manyan injunan da za a yi amfani da su a yankin kudancin kasar da kuma Mogadishu, za su zo a daidai lokacin da ake kokarin fatattar al-Shabaab daga muhimman yankunan da suka mamaye.

Ya yi alkawarin za su yi amfani da kayayyakin, ta yadda za a cimma nasarar mika ragamar tsaron kasar tare da tabbatar da an tsare manyan hanyoyi domin ba da damar zirga-zirgar kayayyakin jin kai da na mutane ba tare da wata mastala ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China