in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata jami'a a Kenya ta yabawa Sin bisa tallafinta a fannin bunkasa binciken kimiyya a Afirka
2018-06-17 15:52:24 cri

Sakatariyar ilimi a majalissar zartaswar kasar Kenya Amina Mohamed, ta jinjinawa tallafin da kasar Sin ke bayarwa a fannin bunkasa binciken kimiyya, da kirkire kirkire a nahiyar Afirka.

Da take tsokaci yayin wata ziyara da ta kai cibiyar hadin gwiwar binciken kimiyya ta Sin da Afirka ko SAJOREC, wadda ke jami'ar raya noma da fasahohin zamani ta Jomo Kenyatta, ta ce sakamakon da ake samu daga bincike na hadin gwiwar sassan biyu, ya samar da damammakin na bunkasa harkokin noma da kare muhalli a Afirka.

Amina ta kara da cewa, cibiyar binciken ta hadin gwiwa, za ta fadada damar da ake da ita, ta hadin gwiwar bunkasa kwarewa, da horaswa, wanda hakan zai wanzar da ci gaban Kenya a tsawon lokaci. Ta ce jami'o'in Kenya sun zamo cibiyoyin kirkire kirkire, da samar da sabbin fasahohi na sana'o'i, wadanda za su agazawa dabarun bunkasa kasar, ciki hadda kudurorin ta na samun ci gaba nan da shekarar 2030, da ma manyan kudurorin kasar guda 4.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China