in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga Rasha da Ukraine da su kai zuciya nesa
2018-11-27 09:51:48 cri

Mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su kai zuciya nesa don kaucewa kara zaman tankiya a tsakaninsu.

Wakilin na kasar Sin ya shaidawa kwamitin sulhun MDD cewa, kasar Sin ta lura da abin da ya faru tsakanin jiragen ruwan kasashen biyu a kusa da zirin Kerch, don haka ta damu da yadda ake kokarin tayar da jijiyar wuyan bayan faruwar lamarin.

Wu ya ce, kasar Sin tana fata tare da yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa, kana su guji aikata duk wani abin da zai kai ga kara tayar da hankali, su kuma warware duk wasu batutuwa ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Jami'in ya ce, har kullum kasar Sin ba za ta canja matsayinta na ganin an yi adalci kan rikicin kasar ta Ukraine ba. Kasar Sin tana mutunta 'yancin ko wace kasa, ciki har da kasar Ukraine, haka kuma ba ta goyon bayan duk wasu bangarori daga waje su sanya baki cikin harkokin cikin gidan kasar Ukraine.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China