in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci Rasha da Ukraine da su guji kara yin fito na fito a kan ruwa
2018-11-27 09:38:34 cri

Babbar jami'ar MDD mai kula da harkokin siyasa Rosemary DiCarlo ta bukaci kasashen Rasha da Ukraine da su guji kara yin fito-na-fito a kan ruwa.

Jami'ar wadda ta bayyana hakan yayin da take yiwa kwamitin sulhun majalisar karin haske, bayan da jiragen ruwan kasashen biyu suka yi sa'in-sa ranar Lahadi a gabar tekun Crimea, ta kuma bukaci kasashen biyu da su guji aikata duk wani abin da ka iya kaiwa ga tashin hankali.

Ta ce, akwai bukatar a hanzarta rage zaman tankiya a tekun Azov da Bahar Asuwad, duba da irin kokarin da aka yi wajen ganin an kawo karshen rikicin shekaru dake tsakanin Rasha da Ukraine.

Kwamitin sulhun ya kira taron ne, bayan kin amincewa da ajandar ganawar ranar farko game da batun da Rasha ta bukata, tana mai cewa, Ukraine ta keta hurumin iyakokin ta na ruwa.

A ranar Lahadi ne sojojin ruwan Ukraine suka ce dakarun Rasha sun bude musu wuta a kusa da zirin Kerch tare da yin awon gaba da jiragen ruwan kasar Ukraine uku, yankin da ya raba Bahar Asuwad da tekun Azov.

Sai dai hukumar tsaron kasar Rasha ta ce, jiragen ruwan kasar Ukraine guda ukun, wato Berdyansk da Nikopol da Yank Kapu, sun keta dokokin iyakar Rasha ta hanyar keta umarnin da jiragen hukumar tsaro ta FSB da wadanda ke tekun Bahar Asuwad dake yi musu rakiya suka ba su. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China