in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sakawa Rasha sabon takunkumi game da batun Ukraine
2017-06-21 09:39:51 cri

A ranar Talata Amurka ta kakaba sabon takunkumi kan kasar Rasha sakamakon manufar Rashar kan batun kasar Ukraine, sashen kula da baitul malin Amurkar ya bayyana cewa, Amurka ta ayyana sunayen wasu daidaikun mutane da hukumomi 38 da take tuhuma.

Mutanen da hukumomin da Amurka ke tuhuma sun hada da wadanda dama tun da jimawa ta shigar da sunayen nasu da suka hada da, wasu jami'an gwamnatin Rasha biyu, da wasu mutane biyu dake aiki da yawun jami'an gwamnatin Rasha, in ji sashin tsimi na Amurkan.

Wadanda Amurkar da rattaba sunayen nasu sun hada da wasu kamfanoni biyu mallakar wasu mutane ko kuma wasu mutane ke gudanar da ikonsu tun a lokacin baya, da kuma wasu daidaikun mutane 11 dake gudanar da al'amurransu a yankin Crimea.

A sakamakon wannan mataki, dukkan wasu kaddarori mallakar wadannan mutane dake Amurka za'a haramta musu amfani ko ta'ammali da wadannan dukiyoyi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China