Dan majalissar zartaswar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Wang Yi, ya aike da sakon ta'aziyya game da rasuwar tsohon babban magatakardar MDD Kofi Annan.
Cikin sakon nasa da ya aike a ranar 19 ga watan Agustar nan, ga babban magatakardar MDD Antonio Guterres, da kuma ministan harkokin wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchwey, Mr. Wang ya bayyana matukar alhinin rasuwar Mr. Annan, yana mai gabatar da ta'aziyya ga iyalan sa.
Tsohon magatakardar MDDr, wanda kuma ya taba samun lambar yabo ta Nobel game da zaman lafiya, ya rasu ne a ranar Asabar yana da shekaru 80.(Saminu)